(ABNA24.com) Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyyeed Aliyul Khaminae ya jaddada bukata ga duk wanda yake son gabatar da kansa don zabe kan wata kujera ta shugabanci a kasar da ya tabbatar da cewa ya cancanci rike matsayin da yak enema.
Jagoran ya bayyana haka ne a karantunsa da manya-manyan dalibansa a safiyar yau Lahadi a gidansa a nan Tehran.
Ayatullahi Kahamina’i ya kawo hidisin manzon Allah (s) wanda yake nasiha ga babbab sahabinsa Abuzar Al-gifari, duk tare da saninsa da fadin gaskiya da kuma tsaron Allah, amma ya ce masa kada ya yarda ya karbi shugabanci ko da tsakanin mutane biyu ne.
A yau ne ake fara rigistar wadanda zasu shiga takarar neman kujeru a majalisar dokokin kasar Iran.
/129